<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>307</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Yara ƙanƙanana, ƙeta sai ku ƙi,
 Daina ƙarya duka, Yesu sai ku bi.

[V2]
 2) Iblis mai zunubi, yara ya ke so.
 Shi zai ƃata hali, yi tsayayya yau.

[V3]
 3) Tsare idanunku duk da kunnuwa,
 Tsabtad da hannuwa, kama harshenku.

[V4]
 4) Yesu mai alheri yana ƙaunarku,
 Yana jin tausayi, yana tsaronku.

[V5]
 5) Yesu ne mai ƙarfi, iko nasa ne,
 Shi zai taimake ku, ku ƴaƴansa ne.</lyrics>
<title>Yara Ƙanƙanana, Ƙeta Sai Ku Ƙi LW307</title>
</song>